ADDU'OIN BIYAN BUKATA

SALLAR BIYAN BUKATA NAN TAKE A DAREN JUMA'A

 A daren Juma'a, ka yi wanka. Ka sa kaya mai tsarki da tsafta kuma mai kyau, Ka yi sallah raka'a hudu da sallama biyu.
Ka karanta a raka'ar farko Fatiha, sai :
ﺩﺎﺒﻌﻟﺎﺑ  ﺮﻴﺼﺑ  ﻪﻠﻟﺍ  ﻥﺍ  ﻪﻠﻟﺍ  ﻲﻟﺍ  ﻱﺮﻣﺍ  ﺽﻮﻓﺍ "Ufawwidu amri ilallah. Innallaha basirun bil ibad" sau dari (100).
A raka'a ta biyu ka karanta Fatiha, sai :
 ﺐﻳﺮﻗ  ﺢﺘﻓ  ﻭ  ﻪﻠﻟﺍ  ﻦﻣ  ﺮﺼﻧ "
Nasrun minallahi wa fatahun qarib" sau 100.
A raka'a ta uku ka karanta Fatiha, sai :
 ﺭﻮﻣﻻﺍ  ﺮﻴﺼﺗ  ﻪﻠﻟﺍ  ﻲﻟﺍ  ﻻﺍ "
Ala ilallahi tasirul umur" sau 100.

A raka'a ta hudu ka karanta Fatiha, sai :
 ﺎﻨﻴﺒﻣ  ﺎﺤﺘﻓ  ﻚﻟ  ﺎﻨﺤﺘﻓ  ﺎﻧﺍ
"Inna fatahna laka fat-han mubinah" sau 100.
Bayan sallama sai ka fada sau 100
 ﺮﻴﺼﻤﻟﺍ  ﻚﻴﻟﺍﻭ  ﺎﻨﺑﺭ  ﻚﻧﺍﺮﻔﻏ
 "Gufranaka Rabbana wa ilaikal masir" Sannan sai ka yi sujuda ka ce sau 100
 ﻪﻴﻟﺍ  ﺏﻮﺗﺍﻭ  ﻪﻠﻟﺍ  ﺮﻔﻐﺘﺳﺍ
 "Astagfirullah wa atubu ilaih"
 Za ka samu biyan bukata nan take da izinin Allah.
Daren Juma'a shi ne ranar Alhamis da daddare. In kuma ya kubuce maka to kana iya yi Jumaa da dare.

SIRRIN FATIHA
Don samun biyan bukata da kuma cimma abin nema,
Ka karanta Suratul Hamd (Fatiha) sau 1011 a daren Juma'a, wato ranar Alhamis da dare, ba tare da rabewa ba ko barci, daga nan ka nemi biyan bukatarka. Ma'ana a zama guda ake so a yi, ba ka soma, ka huta ko ka yi barci, sai kuma ka dora daga inda ka tsaya ba. Allah ya sa mu dace.

ADDU‘AR BIYAN BUKATA
 Wanda yake da wata bukata da ta‘azzara, kuma yake ganin bukatar ta dace dashi sai yayi alwala, ya karanta:-
 Salatin Annabi x100
 Istigfari x100
Fatiha x7
Alamnashrah x79
Qulhuwallahu x1001
 Istigfari x100
Salatin Annabi x100
Sai mutum ya roki Allah har kwana 7. Insha Allah bukata zata biya.

KARANTA KA KARU Sunayen Allah (99) Tare Da Fa'idar Kowane Suna Da Kuma Yadda Za A Yi Amfani Da Shi.
-Allahu (Sunane na ubangiji) shin ne madaukaki acikin sunayensa. Yana daga fa'idar sa idan mutum ya karanta shi sau dubu (1000) Allah zai bashi lafiya ga kowane irin ciwo da ya dame shi.
1. ARRAHMANU. (Sarki mai ba kowa da kowa) Yana daga fa'idar sa wanda ya karanta (100) bayan kowace Sallar farilla ubangiji zai kiyaye shi ga barin rabkana da kuma samun fahimta.
 2. ARRAHIMU. (Mai jinkan muminai). Yana daga fa'idarsa wanda ya karanta shi sau (100) ubangiji zai saki ga66ansa wajen yin ibada.
 3. AL-MALIKU. (Mai gyara bayinsa) Fa'idarsa a karanta shi sau (100) bayan rana tayi zawali domin samun tsarki a zuciya da samun wadata.
4. AL-KUDDUSU ( Tsarkakakke ga barin tawaya). Ana karanta shi sau (100) Allah zai kar6i ibadar wanda ya karanta shi kuma zai yarda da shi.
5. ASSALAMU (Mai shigar da bayinsa muminai aljanna). A karanta shi sau (121) ga mara lafiya. Allah zai bashi lafiya nan take da izinin Allah.
6. AL-MUMINU (Mai bawa annabawa mu'ujiza)
9. AL-JABBAARU (Mai gyara bayinsa) Wanda yake karanta shi a kowace safiya sau (226) ubangiji zai bashi rinjaye ga dukkan azzalumai.
10. AL-MUTAKABBIRU (Tsarkakakken sarko). Wanda ya shi sau (10) yayin da zai sadu da iyalinsa Allah zai azurta shi da 'da namiji.
 11. AL-KHAALIKU (mai samar da halitta) wanda ya karanta shi sau (100) a tsakiyar dare Allah zai haskaka zuciyarsa zai ya bashi kwarjini a fuska.
12. AL-BARI'U  (mahalicci) Yana daga fa'idarsa a karanta sau (100) kullum har kwana (7) Allah zai kiyaye wanda ya karanta daga dukkan cutuka masu wuyar magani.
 13. AL-MUSAWWIRU (mai kyautata halittar bayinsa) wanda ya karanta sau (21) a kullum Allah zai bashi hikima cikin sana'arsa.
14. AL-GAFFARU. (Mai suturce zunuban bayinsa) Wanda ya karanta shi sau (100) bayan sallar juma'a alamomin albarka za su lullu6e shi.
15. AL-KAHHARU (Mai baiwa). Wanda ya yawaita karanta shi ubangiji zai bashi kwarjini wurin al'umma.
 16. AL-WAHHABU (Mai karya makiyan addininsa). Wanda ya yawaita karanta shi Allah zai azurta shi da hakuri da kadan
17. AR-RAZZAKU (mai shimida baiwarsa)   Fa'idarsa wanda yake karanta shi sau (10) kullum bayan sallar asubahi zai samu biyan bukatarsa cikin gaggawa.
18. AL-FATTAHU. (Mai bude kofofin fake). Wanda yake karanta shi sau (71) a kullum Allah zai bashi hasken zuciya.
 19. AL-ALIMU (Masanin komai) Yana daga fa idarsa samun ilimi da sanin ubangiji.
20. AL-KABIDU (mai damke arzikin wanda yaso) Wanda ya rubuta shi sau (4) har kwana (40) Allah zai kiyaye shi daga ciwon ciki.
21. AL-BASIDU (Mai ciyar da bayinsa) wanda ya karanta sau (10) bayan sallar walha ubangiji zai bude masa kofofin wadata.
22. AL-KHAFIDU (mai kunyata makiyan addininsa) wanda ya karanta shi sau (500) Allah zai isar masa da duk abinda ya dame shi.
23. AR-RAFI'U (Mai daukaka waliyansa) Wanda yake karanta shi sau (70) Allah zai kiyaye shi daga zaluncin azzalumai.
24. AL-MU'IZZU. (Mai bada mulki). Wanda yake karanta shi sau (40) a kullum Allah zai bashi kwarjini.
25. AL-MUZILLU (Mai ta6ar da azzalumai) Wanda ya karanta shi sau (75) Allah zai ku6utar dashi daga dukkan hadari.
26. AS-SAMI'U (Maji rokon bayinsa). Wanda ya karanta ranar juma'a bayan sallar walha zai zamo mujabu da'awati.
 27. AL-BASIRU (Mai ganin bayinsa) Wanda ya karanta ranar juma'a sau (100) Ubangiji zai bashi basira.
 28. AL-HAKAMU (Wanda ba'a juyar da hukuncinsa) Wanda ya karanta shi a karshen dare a bisa tsarki Allah zai kyautata badininsa sa zahirinsa.
 29. AL-ADALU (Ya tsarkaka ga barin zalinci) Wanda ya rubuta ranar juma'ah ko daren juma'ah sau (20) Allah zai hore masa dukkan halitta.
 30. AL-LADIFU (masanin boyayyen lamari) Wanda ya karanta shi sau (133) Allah zai yalwata arzikinsa.
31. AL-KHABIRU (Babu abinda yake 6uya ga halittarsa) Wanda ya karanta sho sau (7) kwana (7) Allah zai ku6utar da shi daga wanda yake tsare da shi.
32. AL-HALIMU (Mai rangwame) Wanda ya rubuta shi a takarda ya wanke da ruwa ya shafa kayan sana'arsa zai samu albarka a cinikinsa.
33. AL-AZIMU (mai girman kadari) Wanda ya karanta shi a kullum sau (12) Allah zai kiyaye shi daga dukkan abin ki
34. AL-GAFURU (Mai sitirce bayinsa). Wanda ya rubuta shi ya shayar da shi ga wanda hauka ya same shi zai warke nan take da yardar Ubangiji.
35. ASH-SHAKURU (Mai bada lada). Wanda ya rubuta shi ya shayar da da shi ga mai jiki zai samu saukin jikinsa.
36. AL-ALIYU. (Mai isa matuka). Wanda ya rubuta shi ya shayar da shi ga yaro karami Allah zai raya wannan yaron ya kai har girmansa
37. AL-KABIRU. Mai girman sha'ani) Wanda ya karanta shi kullum sau (1000) Ubangiji zai maida shi akan mulkinsa
 38. AL-HAFIZU. (Mai isa matuka) wanda ya karanta shi a wurin da yake jin tsoro Allah zai kubutar dashi
39. AL-MUKITU. (mahaliccin abinci). Wanda ya karanta shi akan tur6aya kuma ya shaki turbayar zai samu rimjaye a dukkan lamarinsa.
40. AL-HASIBU. (Mai baiwa bayinsa). Wanda ya karanta shi sau  (27) zai rinjayi makiyansa.
41. AL-JALILU. (Mai girma akan komai). Wanda ya karanta shi zai samu kwarjini a cikin jama'a.
42. AL-KARIMU. (Mai baiwa). Wanda ya karanta shi lokacin da zai kwanta Allah zai sanya shi cikin waliyyansa.
43. AR-RAKIBU. (Mai tsinkayarayyukan bayi). Wanda ya karanta shi ga mai nakuda sau (7) zata haihu da gaggawa da izinin Allah.
44. AL-MUJIBU. (Mai amsa rokon bayinsa).   Wanda ya karanta shi a kullum Allah amsa rokonsa.
45. AL-WASI'U. (Masanin komai). Wanda ya karanta shi Ubangiji zai kiyaye shi da yin hako ga bayin Allah.
46. AL-HAKIMU. (Mai isa cikin hikima). Wanda yake yawan karanta shi Allah zai bude masa kofofin hikima.
47. AL-WADUDU (Masoyin muminai) Wanda ya karanta shi sau (1000) zai sai soyayyar ubangiji (S.W.T)
48. AL-MAJIDU (Mai cikakkiyar sifa). Wanda ya karanta shi yayin 6ude baki Allah zai kiyaye shi ciwon albaras.
 49. AL- BA'ISU (Mai aiko manzanni) Wanda ya karanta yayin da zai kwanta sau (100) Allah zai bashi hasken ilimi.
50. ASH-SHAHIDU. (Masanin dukkan komai). Wanda ya karanta shi a kowane lokaci Allah zai tabbatar da shi akan gaskiya.
51. AL-HAKKU. (Matabbacin samuwa). Wanda ya karanta shi Allah zai sanya arziki a hannunsa Zan Cigaba insha Allah

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

MATA KAWAI